
Lawaliabdulmudallib
2025/08/19 09:27
BAYANI AKAN WANNAN BULL RUN DIN
ku dage ku karanta har qarshe, sannan kuyi sharing da tagging friends dinku a comment
Yadda Bond da Bond yield yake aiki.
Yana daga cikin abinda kesa a shiga bear market koh bull run. Duk wanda ya saurari live din jiya nayi bayani akansa, haka a Trading square shima.
Yanzu bashin da kekan US yana dayawa, kuma mutane sun fara jin tsoron cigaba da bawa US rancan kudi, saboda tsoron cigaban tashin inflation( tunda dama saboda tsoron inflation dinne yasa suke rantawa US kudin, kaga indai US bazasu iyaba, dole sai dai a qara musu % din bond yield din, wanda hakan zai iyawa US tsadan biya).
Solution dayace ta ragewa US, shine su fara QE, indai sun fara QE, zaisa bashin da ake binsu ya ragu, sannan bond yield( % na kudin riba da suke bawa mutane) shima dole ya ragu, in hakan kuwa ya faru, inflation zai qara sama, wanda hakan zai tilastawa masu wannan kudin su fara niman alternative source of hedge against inflation, wannan ne zaisa dole suyi developing risk appetitite, ta considering risk on assets, irinsu stock da, crypto .
Uwa uba, yanzu GPD din US a negative yake, wannan ka iya sa tsoron shiga recession, saboda export dinsu ya ragu, tunda dama kamar yadda na nake fada, majority na products din da US suke sai dawa duniya, daga china ake bugasu, yanzu kuma an sakawa products din china haraji a US kamar yadda itama china ta rama, sai dai abin yafi illata US. Shi kuma powell tsoronsa daya shine, baisan yayi cutting rate abin yasa inflation ya qaru sosai, saboda a wannan gabar ake yanzu , due to Tarrif .
Yanzu matsala hudu ke gaban US :
1. Inflation
2. Recession ans GDP yana qasa
3. High debt da High bond yield
4. Unemployment rate increase.
In akai cutting rate, inflation zai saurin qaruwa, saboda tarrif, inkuma akai increasing rate, zai qara watsa GDP din US, wanda hakan shima already andade ana hasashensa , zai iya fin inflation karfin zuwama, sannan zaisa a qara samun rashin aikinyi, sannan government bazasu iya samun kudi sosai ba, saboda companies din qasar baswa expanding, hasalima shrinking(matsewa) suke, saboda ba daman ranto kudin da zaisa a iya qara producing more goods din da zaisa a sanu qarin ribar da government zata iya taxing, saboda kaso .ai tsoka daga source na revenue din US yana zuwa daga Tax ne, kaga kuwa indai company din qasa basu samu wal-walan kudi ba, toh ba halin qara producing.
QT(Quantitative Tightening) din da akai daga 2022 zuwa yanzu shine yaja, saboda anyi over fighting inflation, daga 9%, zuwa yanzu da yake 2.7%, Powell yaso inda ya fara cutting rate a 2024 ya cigaba har izuwa yanzu, amma tarrif din da Trump ya fara yasa yaji tsoron cigaba da hakan, wanda hakan shine daidai.
Yanzu government bata da daman cigaba da QT, saboda masu ranta mata kudin yawanci sun fara nuna alamar a qara musu bond yield %, saboda tsoron tarrif. Wannan yasa dole US ta samun hanyar rage wannan yield bond % din, hanyar ka da ake amfani dashi shine printing din kudi, tunda dama basu da kudin, da'ace suna dashi, da basu nime rancen ba.
Shi kuma printing dun kudin zaisa inflation ya qaru, saboda wannan dalilin ne yakesa masu kudi dole suma su shigo stock market da crypto a dama dasu inba haka ba, su zasuyi asara, tunda government sun rage yield bond, kuma yield bond bai isa ya iya karawa da inflation din dake zuwaba, wannan yakesa a samu bull run, kowa dole yabi, da mai kudi da mara kudi.
Kamar yadda na dade ina fada muku, bull run zaizo, da yazo tun daga 2024 da aka fara rate cut, amma saboda tsarin trump na tarrif, shine dalilin dayasa Powell shikuma yaqi cutting rate, da ace ancigaba da cutting rate din, da market din yayi bull run irin na 2020 zuwa 2021, amma wannan karan sai yayi kamada na 2017, dukda ya dan banbanta dana 2017 saboda , ba'a samu irin delayance din da aka samu a wannan cycle din ba, so wannan ya danyi kamada na 2017, amma akwai banbanci sosai, saboda interest rate din 2026 ( wanda yayi dai dai da 2024 na wannan cycle din)
Cigaba 👇👇

1. BTC (Bitcoin) shine token na farko da aka fara samuwar a duniya akan fasahar blockchain. Yayin da HBAR na kamfanin Hedera shine token na farko da aka fara samarwa a duniya akan fasahar Hashgraph. Mutane da yawa suna mamakin ace anyi token ko NFT ba akan fasahar blockchain ba, eh yana yiwuwa a yanzu akan fasahar Hashgraph. Yayin da HOT shine token na farko akan fasahar Holochain.
Muna da Distributed Ledger Technology, ko DLT, da yawa a duniya. Amma babu wanda aka fi sani kamar blockchain technology. Blockchain daya ne daga cikin DLTs wato "Distributed Ledger Technologies".
2. Bayan blockchain akwai Hashgraph, shima Distributed Ledger Technology ne wanda yanzu haka yake bin bayan fasahar blockchain wajen sanuwa a duniya, token na farko akan sa shine HBAR token na Hedera Network.
3. Na uku, akwai "Directed Acyclic Graph" ko DAG shine DLT ne.
4. Na hudu akwai Holochain, shine Distributed Ledger Technology ne irin Blockchain technology. An samar da token din HOT akan sa a 2020 a matsayin na farko.
5. Sai Tempo ko RADIX shima DLT ne, amma ban san wani token da aka gina akan wannan fasahar ba a yanzu.
Duniya tafi sanin blockchain a bangaren Distributed Ledger Technology, tare da cewa ya dauke da kalubale masu yawa ta wasu wuraren, a yanzu a bangaren DLTs an fara fahimtar fasahar Hashgraph da irin yadda yake da tsaro da "Gossip about Gossip Protocol" dinsa da kuma "Vitual Voting" a matsayin hanyoyin da yake tattare bayanai da kuma watsa su ko ajiye su.
Hashgraph yana cigaba da bayyana a bangarori daban daban na duniya tun bayan aiyukan da Turawan Hedera Network suka fara aikin samar da tokens, NFTs akan fasahar Hashgraph technology ba Blockchain technology ba.
Wasu masana suna ganin fasahar blockchain tana dauke da kalubale sosai, suna kallon fasahar Hashgraph a matsayin solution. Yanzu haka duniya tana samar da RWAs da kuma tokens da NFTs akan fasahar Hashgraph sabanin abinda aka saba gani na kirkiran tokens akan fasahar blockchain.
Kamfanoni irin su Google, IBM, Grayscle, Apple suna daga cikin manyan kamfanonin da suke goyon bayan amfanin da fasahar Hashgraph a yanzu, inda suke zabi zama cikin Governance council ne wadanda suka fara bayyana fasahar Hashgraph, sune Hedera Network.
Ko a nan Nigeria a yanzu haka muna kan kokari wajen ganin mutane sun fahimci fasahar Hashgraph, bayan Blockchain da aka fi sani.